• muhsinu 5w

  MU FARKA (A POEM)

  Ance idan kaga gemun danuwan ka ya kama da wuta
  To kayi kokari ka shafa ma naka ruwa

  In yakasance gemun danuwan ka na ci da wuta
  Kuma kaima naka ya kama da wuta

  Naka yakamata ka fara kashe ma wuta
  Sannan ka shafa ma nashi ruwa

  America na can tana ci da wuta
  Mu ma kasar mu (Nigeria) tana nan tana ci da wuta

  Amma kokarin zuwa muke mu kashe musu wuta
  Alhalin muma muna da bukatan taimakon me ruwa

  Meyesa muke pretending Kaman ba abunda ke faruwa?
  Alhalin kullun abun yana karuwa

  Ko don ita (America) kasar turawa ce?
  Wadda take wayayyar da ta zarce duk wata kasar da ke neman tazarce

  Shiyasa muke koyi dasu a komai domin ace mun zarce
  Ace muma ga wayayyu a idon duniya mun zarce..

  Toh in bah aka ba meyasa bamu goyon bayan palastinu?
  Bamu maganan Syria da yan yemen in mu
  Wa’inda kullun ake rusa ma gidajen su

  Ni ba ina fada da taimaka ma mutanen mu (bakake)
  Sedai ina kira musan ciwon kawukan mu

  Yanda muke cika social media da batun bakaken mu
  Kamata yayi mu cika ta da maganganun nahiyoyin mu

  Tanan kadai zamu nuna waye wan mu
  Tanan kadai zamu nuna mun san ciwan ka wunanmu
  Gaskiya ya kamata mu farka!

  ©muhsinu31052020