• elhuzzy 5w

  Shekaru biyar da suka gabata,
  Ita ce kadai a raina.

  Bazan iya misalta yadda nake sonta ba,
  Abun ya wuce tunanina.

  Gani nake rayuwa babu ita,
  Zan iya rasa raina.

  Ko da ta mini laifi,
  Nakan daure domin ita ce farin cikina.

  Rana kwatsam! Ta juya mini baya,
  Abun mamaki wai ta gujeni.

  Hakan ya haddasa mini matsaloli,
  Kullum ina cikin tunani.

  Ji nake babu ita,
  Nima babu ni.

  Na rasa yadda zanyi,
  Son ta dashi Allah ya jarrabeni.

  Ita ce mace ta farko,
  Da na fara so a rayuwata.

  Farkon haduwarmu,
  Nayi tunanin cewa zata kawo farin ciki a rayuwata.

  Kamar da wasa,
  Ni da ita muka zamo tamkar jini da hanta.

  Dalilinta yasanya ban kula kowa,
  Burina shine ta zamo matata.

  Amma yau naje gidansu,
  Ta mini korin wulakanci.

  Nace ta tsaya ta saurareni,
  Tace mun bata da lokaci.

  Wayyo Allah! Ya zanyi,
  Rayuwata ta shiga kunci.

  Ji nake kamar zan mutu,
  Banda sauran numfashi.

  ©Huzzy